Nono halitta ce a jikin mace wadda take jan hankalin namiji kwarai da gaske, musamman nonon daya kasance cikekke, ma’ana bul-bul babu yamushewa a tattare dashi.

Don haka ya zama dole mace ta gyara shi yadda zata karawa kanta kima da daraja a wurin jinsin maza da jinsin mata. Bisa wannan dalili, akwai abubuwan da zaki nema wajen tabbatar da ganin nonon sun kai matakin da ake bukatar ya kasance.

Zaki nemi kayan hadi kamar haka :

– Garin habbatus sauda
– Garin yayan hulba
– Garin alkama
– Gyada
– Ridi
– Farar shinkafa
– Busassahen karas
– Madara

Yadda Za’a hada :

Zaki samu garin habbatus sauda da garin yayan hulba da garin alkama da gyada da ridi da danyar shinkafa wato Wanda akeyin tuwo da ita da busassen karas duk ki dakasu waje daya ki dakasu su zama gari sai ki ajiyeshi kina diban kadan kina sha da madara peak ko nonon saniya, kuma zaki sha da dare wato sa’o’i biyu (2hours) kafin barci da kuma sa o i biyu (2hours) bayan tashi daga barci kiyishi kafin sati daya zakiga canji yana ciko da nono sosai kuma su kara girma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *