Mata da yawa suna son babban kugu domin yana daga cikin abubuwan da suke jan hankalin maza, musamman a wannan lokacin na karfin sha’awa a wurin samari. Wannan yasa kusan kowacce mace take son ta mallaki babban kugu.

Girman kugu yana da matukar fa’ida sosai a wurin mace ta fuskoki da bangarori daban daban, saboda yana saka kyawu da farin ciki ga ma’abociyar sa, da kuma sanya cikar diri na halitta

Don haka duk macen da take son duwawunta suyi girma su zama manya-manya kamar an hura su, ko kuma take son taga nonuwanta sunyi manya-manya kuma ba za su zube ba, sai ta samu kayan Zaki na gona suna da matukar amfanin a jikin mace, ki daure ki dinga yawan shan su, ga mahadan:

Abarba
Madara
Kankana
Lemo
Suga
Gwanda

Hanyar Da Za’ayi Wannan Hadi:

yar’uwa ki sami kankana ki yankata sai ki sami bilenda mai kyau ki murjeta kamar an markada, itama abarbar kiyi mata haka, ki cire bakin idonta, gwandar ki markade ayar kuma ki dameta kamar fura, lemon kuma kiyi masa sala-sala, sannan a saka a cikin bilenda a matse shi, bayan kin gama matse su, sai ki tace su ki saka sukari, da madara, sai ki dama, sai ki sa a firji ko ki daure a Leda ki sami kankara ki dora akanta, idan yayi sanyi sai asha.

Zakiyi matukar mamakin yadda jikin ki zai sauya cikin kankanin lokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *