Ku nemo lemon tsami, Kurkur da kuma zuma mai kyau.
Ta wanke fuskarta sosai da ruwan dumi, ta goge da tsumma mai tsafta sannan ta tsaga lemon tsamin gida biyu, ta murje fuskarta dashi (akwai zafi ka’dan). Sai bayan kimanin minti biyar ta tashi ta wankeshi da ruwan dumi.
Sannan ta zuba garin kurkur din nan rabin cokali acikin zuma cokali biyu, ta gauraya ta shafa akan fuskar, ta barshi zuwa kamar minti 5 sannan ta wanke. Idan ya bushe ta shafa man zaitun.
In sha Allahu kurajen fuskar zasu mutu, kuma duk wani tabo ko baqi-baqi zai washe daga fuskarta.