Bushewar gaba tana daya daga cikin alamun rashin ni’ima ga mace. Don haka ya zama kusan wajibi ga mace ta magance wannan matsalar.
Dabino yana taka muhimmiyar rawa a jikin dan adam ta bangarori da dama, musamman wannan bangare na bushewar gaba, bisa dalili na maganin da yake dashi ga lafiyar dan Adam, da sauransu.
Zaki nemi kayan hadi kamar haka :
– Asuwankin mata
– Gyadar mata
– Dabino
– Kanunfari
– Aya
– Mazarkwaila
– Idon zakara
– Madara peak
Yadda Za’a Hada :
Zaki samu wadannan kayan hadin sai ki hadesu guri guda ki ta dakawa har su hade sai ki dunga diba kina zubawa a madara kina sha.