Sha’awa halitta ce mai karfin gaske a jikin dan adam, domin tana daga cikin alamu da za’a gane mutum yana cikekkiyar lafiya a bangarori da dama, tun daga lafiyar data shafi jiki har zuwa wacce ta shafi biyan bukatar iyali.

Mata da dama suna korafi akan cewa basu san mecece sha’awa gaab dayanta ma, domin basu da ita a jikinsu, kuma basa jin sauyin yanayi a jikinsu a lokacin da wani abu ya faru, ko kuma wani namiji ya kusance su.

Domin Kasancewa cikin dauwamamiyar ni’ima da sha’awa, sai mace tayi amfani da wannan hadi wajen samun kyakkyawan sakamako da yardar Allah.

Zaki nemi kayan hadi kamar haka:

– Garin habbatus sauda
– Garin yansun
– Man yansun

Bayanin yadda za’ayi wannan hadi

Zaki samu garin habba da garin yansun ki hadesu guri daya ki tafasa idan ya tafasa sai ki tace ruwan ki zuba man yansun din a cikin ruwan ki juya sai ki dunga sha, ki yawaita shan kuma zaki sha na tsawon sati biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *