Ciwon ciki ko ciwon mara yana daya daga cikin manyan ciwo na jinsin mata, kasancewar suna yin al’ada. Yadda budurwa ko matar aure mai fama da wannan matsalar, ki samu wadannan abubuwan kamar haka :
1. Garin hulba
2. Garin habbatussauda
3. Garin kustul Hindi
Sai ki hadasu waje daya sannan ki zuba ruwa da zuma a ciki sai ki dafasu, idan ya dafu daga nan ki ajiye wannam ruwan da safe ki debi karamin kofi kisha kafin kici komai,anaso ki dafa wanda zai miki sati daya kafin ya kare kin huta da wannan matsalar Insha Allah.
WARIN GABA:
Ga Kadan daga cikin Abubuwan dake sanya gaban mace yana wari :
1. Tafiya babu wando.
2. Rashin sanya takalmi, koda kuwa acikin gidane.
3. Dadewa akan masai (toilet).
4. Rashin canza pant da wuri.
5. Yawaita cin danyar albasa.
6. Istimna’i (Masturbation) wato mace ta biyawa kanta buqata ta hanyar wasa da gabanta.
7. Tsarki da ruwan sanyi.
8. Rashin aske gaba, dadai sauransu.
YADDA ZA’A MAGANCE WANNAN MATSALA :
1.Ki dinga tsarki da ruwan dumi.
2. Kidinga yawan canza wando a kullum kamar sau 2 ko 3.
3. Ki rage cin danyar Albasa.
4. Aduk lokacin da kika kama al ada ki dinga wanke gabanki da ganyen magarya da farin almiski.
5. Sannan ki daina tsugunawa akan masai (toilet) kina daukar tsawon lokaci.
6. Ki yawaita aske gabanta duk sati 1 ko 2.
7. Sannan kada ki rinka saka pant da jikar ruwa ajiki bayan kinyi tsarki ki goge kafin ki sashi
8. Kada kirinka barin iska tana shiga farjinki musamman matan Aure wasu suna kwanciya babu wando kuma panka ko easy sunayi ki sani iska ko sanyi da wuri suke jawowa Mace illah a gabanta…