Kuraje wasu alamu ne na cuta dake tattare a jikin halitta. Kasancewar sa a jikin dan adam, musamman jinsin mace, yakan haddasa mata rashin kyawun gani a fuskarta, da kuma muni a fuska.

Don haka ya zama dole mace ta kasance ta gyara fuskarta domin cikar kyawunta, da kuma tabbatar daya haskaka ta a wuri da kuma idon al’umma.
I
– Ki samu ganyen bedi, sai ki hada shi da kurkur, sannan sai ki shafa a fuskar, se ki jira tsawon minti 15, sannan ki wanke da ruwan dumi.

– Zaki a iya shafa markadadden dankalin Turawa a kan tabbunan dake a fuskar da kuma inda kurajen suke. Hakan na magance kurajen fuska, sannan ya hana su sake fitowa.

– ki daka tafarnuwa sai ki shafa a fuskar ki duka. Tafarnuwa tana da wari, amma tana gyara fuska, sannan ta magance tabon fuska.

– ki hada karas da tafarnuwa da zuma sai a shafa a fuska na tsawon minti 20 kafin a wanke.

· ki samu hodar ‘baking soda’, sai ki hada ta da ruwa, sannan ki shafa a fuska zuwa minti biu ko uku, daga nan ki wanke fuska da ruwan dumi.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *