Wasannin ma’aurata Iri-iri ne. Suna ƙara danƙon soyayya da samun biyan bukata. Suna sa biyayya har ma da mallaka
Rashin su kuwa, na sa ɗaya daga cikin ma’aurata ya zauna cikin sha’awa, da kunci, da rashin natsuwa, har ma ya kai ga ƙiyayya. Ko ma rabuwar ma’aurata.
Ire-iren wasannin sun haɗa da shafa wasu sassan jiki a hankali. Yin sumba ( Kiss) na labba, da runguma , da yin amfani da baki/harshe a wasu sassan jiki. Da hura iska a kunne. Da dai sauransu.
Amma fa runguma da sumbata ba za su yiwu ba. Sai dai da wanka, wanke baki da fesa turare.
Idan miji/ ko mata ta ji kana wari. Za ka ga kawai tana ƙin kusantar ka, balle wasanni.
Idan aka jarrabe ki da mijin da bai iya wasa ba. Ko matar da ba ta iya wasa ba. To yakan sa a ji an gaji da juna.
HANYOYIN KOYAR DA WASANNI
1- Ban da ɓata rai, da ƙorafi , da nunawa wanda ba ya wasan shi/ ita ‘yar ƙauye ce.
2- Kai/ke mai koyar da wasan zai fara ne da maganganu masu gayyato sha’awar mijinki. Da yaba masa yana burge ki a shimfiɗa ko da ba hakan ba ne kuwa.
3 – Mai koyarwar ya dinga ɗauko hannun miji/ mata yana sawa a inda yake so a jikinsa. Domin shafa…
4 – Ki kai abin da kike so ga bakin mijinki. Kai ma ka kai abin da kake so ga bakinta..
5 – Ba da labarin irin daɗin da ake ji idan akai Miki/maka abu kaza.
6 – Bayar da umarni, amma fa cikin lumshe ido da sigar buguwa/maye na kalar wasan da ake so ga mijinki ko matarka. Kallon wannan yanayin naka, zai sa nan da nan a yi abin da aka umarta.
Zai fi kyau ga ma’aurata ma a kowanne lokaci za ku rabu, ko ku ka hadu. To a fara da sumbatar juna.
Nana Aisha ta ce: “Manzon Allah (S.A.W) yana sumbatar matarsa idan zai fita. (Abu-Dawud).
A ƙarshe ya zama tilas ga ma’aurata, su kula da gabatar da wasanni kafin shimfiɗa. Domin da yawa ma’aurata ba sa samun gamsuwa in babu wasanni. Hakan na haifar da matsaloli da yawa ga su Ma’aurata.