Ina mata da maza wadanda kuzari bai ishe su ba sannan kuma basa jin karfin jikin su, to wannan wata damace ta samu idan kuna san samun kwari da kuzari, sai kuyi wannan hadi ku gani.

Abubuwan da za’a nema :

– DABINO.
– NONON AKUYA.
– ZUMA.
– CITTA.

A samu dabino mai kyau, a tabbatar an gyara shi saboda yawancin dabino ana samun kwari a ciki.

Nonon akuya anaso a samo wanda aka tatsa a gaban mutum dan an samu ingantacce kuma tsaftaceccen nono. Sai a zuba dabinon da aka gyara a cikin nonan akuyar, ana bukatar ya samu kamar awanni goma (10) idan da hali ayi da dare sai ya kwana, ma’ana da safe dabinon ya jika acikin nono akuyar.

Ana so akai a markade amma kada a zuba ruwa a cikin markaden, idan an gama sai a dauko zuma, amma anfi san farar saka sai dai in ba’a samu ba sai ayi da ko wacce a zuba zumar a ciki ki a juya.

Ita kuwa citta garinta za’a samu mai kyau wanda aka san babu wani mis a ciki, ko kuma a daka shi domin hakan yafi sauki. Sai ana shan wannan hadi ko kana shan wannan hadi zaku ga yadda kuzari zai samu da yarda Allah.

Haka za’a na sha kullum da safe har lokacin da zai kare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *