Wacce take so jikinta yayi kyau taga tana cikowa, fatarta tayi kyau da haske, to ga wani sirrin.

Zaki nemi kayan hadi kamar haka ;

– Lemon Zaki
– Lemon tsami
– Kwaiduwar kwai
– Zuma mai kyau

Bayani Game Da Yadda Zaki Hada ;

Zaki samu wadannan kayan hadin sai ki matse lemun zakinki da lemun tsami a wajen daya, sai ki fasa kwai guda daya kiyi amfani da kwanduwar kwan, sai ki sa ta a cikin ruwan lemun nan, ki zuba zuma mai kyau babban cokali uku, sai ki juya ki sha. Amma da safe zaki dunga sha kafin abinci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *