Yar uwa warin gaba matsala ne, wasu yana zama sanadiyar rabuwar aurensu, saboda wannan dalili yar uwa ya zama dole kiyi iya kokarinki domin magance wannan matsala.
Don magance wannan matsalan zaki bi hanyoyi kamar haka ;
– Hanya ta farko ita ce, Wanke gaba da gayen magarya ko miski ko kanunfari ko alim ko kuma bagaruwa musamman bayan daukewar jinin al’ada.
– Hanya ta biyu kuma ita ce, sanya pant busasse.
– Hanya ta uku ita ce, Tsarki da ruwan dumi.
– Hanya ta hudu ita ce, Tafiya da pant
– Hanya ta biyar, Tafiya da takalmi a kafarki, koda a cikin gida ne.
– Hanya ta shida, Rage yawan dadewa akan masai/toilet.
– Hanya ta bakwai, Rage yawan cin albasa.
– Hanya ta takwas, kuma ita ce, Rage yawan amfani da tafarnuwa.