Kasancewar mura ko kuma a takaice ciwo nau’in sanyi yana haddasa babbar matsala a jikin dan adam, ta hanyar kashewa mutum lakar jiki, da kuma yawan samun rashin kuzari don aiwatar da ayyukan yau da kullum.
A bisa wannan dalili ne yasa zamu kawo muku wata hanya daga cikin hanyoyin da za’a bi domin ganin an tabbatar da wanzuwa da dorewa ta lafiya, da kuma samun kariya daga cututtukan da suka shafi sanyi.
Don haka duk wanda yake fama da matsalar sanyi mai ratsa jiki, mura, tari ko kuma zafin makoshi sai ya nemi wadannan abubuwa kamar haka :
1. Lemon tsami
2. Citta
3. Zuma
4. Tafasasshen ruwa
Atanadi ruwa tafasasshe sai a kankare cittar sannan sai a sanya cittar cikin ruwan sai a matsa rabin lemun tsami asanya zuma cikin karamin cokali sai bayan ya jiku kamar minti 10 zuwa 15 sannan arinka sha kamar ana shan shayi.
Za’a rinka yin irin wannan hadin anasha kullum har tsawon sati daya insha Allahu za’aga abin mamaki
Allah yasa mu dace. Ameen