Da yawa mutane suna neman magani ne,amma sai su tsallake asalin magani su tafi neman wani abu daba bisa rashin sani.

A yau insha Allahu zan sanar daku 2 daga cikin amfanin shan Garin kaninfari da madara ta ruwa

1. Yana magance matsalar saurin kawowa

Matsalar saurin kawowa matsala ce da take damun mafi yawan magidan ta a wannan lokaci musamman ma wadan da basu da manyan shekaru,wanda hakan a tare dasu babbar illa ce da kuma barazana a zamantakewar su da abokan zaman su.

2. Matsalar infection.

Infection wanda aka fi kira da sanyin mara,shima yana daga cikin ciwokan dake dakun jama’a mata da maza, yan mata, da zawarawa.

Shin ta wacce hanya zaa iya magance wadannan matsaloli da kaninfari ?

Za’a nemi :

1. Garin kaninfari
2. Madara ta ruwa

Za’a samu garin kaninfari rabin karamin chokali a zuba a ciki karamin kofi na madara ta ruwa a juya sosai sannan ana sha sau daya a rana har na tsawon kwanaki 7, ma’ana sati daya.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *