Ana cin dabino kwara bakwai kullum da safe idan an yi kusan haihuwa. Wannan yana hana wa macce yawan zubar da jini lokacin haihuwa da iznin Allah.

Gudawa:

A na daka shi garin dabinon a sa shi a ruwan zafi a sha Inshaa Allahu yana tsayar da gudawa.

Samun Kuzari:

A na cin dabino guda uku, a sha zuma Cokali daya da safe da yamma.

Ana hada garin dabino da zuma da man zaitun a shafa a fuska, awa daya sai a wanke fuskar da ruwan zafi wannan yana saurin gyara fuska. Bincike ya nuna cewar yawaita cin dabino na hana kamuwa da ciwon daji (wato ‘Cancer’) ko wacce iri.

Haka Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce ‘Dabinon Ajuwa yana maganin dukkan cututtuka, kuma duk ranar da mutum ya ci irin wannan dabino na Ajuwa (wato wanda ake tsinkowa daga birnin Madina, wanda aka tabbatar a gonarsa ake samun dabinon), babu wata cuta da za ta same ka a wannan rana ko sammu ko kuma wani sihiri.’

Yadda za a yi amfani da shi wajen warkar da ciwon Nono ga wadda ta haihu kuwa shi ne a rika cin kwayar dabino guda bakwai, asha man tafarnuwa karamin cokali sau daya a rana har na tsawon kwanaki uku.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *