Yadda zaka magance matsalar inzali da wure shine ta hanyar amfani da maganin gargajiya na asali wanda babu wani chemicals ko kuma sinadarin da zai zama mai illa ga ga lafiyar dan Adam a cikin sa, domin samun ingantaccen kuzari marar yankewa, ma’ana na har abada.
Wannan hanya zata magance maka matsalar raunin gana saurin inzali dàttin mara.
– Citta mai kogo
– Namijin goro
– Tafarnuwa
– Kanumfari
Yadda za’a hada shine ; idan aka samo namijin goron sai a barshi ya bushe, sannan a samu yayan citta mai kogo, sai a samu tafarnuwa da kanumfari a hada su wuri guda a daka su sosai suyi laushi.
Bayan an kammala wannan hadin sai ana zubawa a cikin zuma ana shan chokali 1, sau biyu a rana.
Za’a kuma iya sha a cikin nono ko madara ta ruwa chokali 1, shima sau biyu a rana.
Ana amfani da wannan hadin har tsawon sati 2, amma kafin a fara ganin aikin sa, sai anyi tsawon kwana 3 zuwa Kwana 5 ana sha, domin yana bin jiki ne.