Akwai abubuwa masu tarin yawan gaske da suke haddasa rashin gamsar da maigida, wata macen bata san cewa bata gamsar da maigidanta ba sai dai kawai taga yana wulakantata yana nuna mata rashin kauna.

Saboda duk matar da bata gamsar da mijinta to dole ne ya gallaza mata, dole ne yayi mata uku ba, dole ne ya wulakanta ta duk irin dimbin soyayyar da miji yake yi miki kuwa ba zata yi tasiri ba.

Don haka sai ki gyara, kaima idan ka gani ka fadawa matar ka domin ta gyara, hakan zai amfanar daku gaba daya.

1. TAFIYA BABU TAKALMI A CIKIN GIDA : Wannan ba karamin jefa mace yake cikin hadari ba, don yana rage mata ni’ima sosai ko da kuwa kina da wadatacciyar ni’ima rashin sanya takalmi zai iya cutarda mijinki. Don haka sai ayi hattara kuma a kiyaye.

2. SAMUWAR FASO KO KAUSHI : Shima yana haddasa wa mace rashin gamsar da maigidanta, sakamakon wasu kwayoyin halitta da suke raguwa. Bisa wannan dalili, ya kamata mata suyi kokari wajen kiyaye wa.

3. JINKIRTA WANKA HAILA : Don a yadda akeso idan mace ta gama al’ada, tana gamawa ta sami auduga tasa turaren miski tasa a farjinta zuwa wani dan lokaci ta cire tayi wanka. Amma jinkirta hakan yana sanya mace tana warin jiki.

4. RASHIN CIN ABINCI MAI GINA JIKI : Shima yana haddasa wa mace rashin ni’ima. Domin abinci mai gina jiki yana taimakawa wajen samar da dauwamamiyar ni’ima a jikin mace.

5 AMFANI DA MAGUNGUNAN MATA : Yawan yin amfani da magunguna na mata shima yana haddasa wa mace bushewa, saboda yana matso miki ruwan jiki ne da tsiya, wanda yau da gobe kuma zai kare shikenan kin shiga matsala idan baki cin abinda zai kawo ruwan, ayi hattara! Bako wanne magani zaki dauka kiyi amfani dashi ba, ki tabbatar da ingancinsa kuma kin tabbata babu sihiri a ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *