Da farko dai ana bukatar mace ta gujewa ruwan sanyi saboda Illa ce a gare ta.
Ko da yaushe ana bukatar mace ta kasance mai amfani da ruwan dumi wajen tsarkin fitsari, da kashi, da haila (al’adar), da tsarkin jinin biki, sannan a cikin ruwan dumin a dan kada alumu kadan kadan a ciki.
Idan mace tana fama da
– Warin farji
– Fitar farin ruwa a cikin farji
– Kuraje farji
– Karnin farji
– Kumburin farji
– Kaikayin farji.
– Ko kina jin wani Abu yana yawo a farjinki ko kuma datti ya shiga, kin barshi har ya dankare kin rasa yadda zakiyi dashi.
Abinda ya kamata kiyi shine neman magani wanda zai kore miki wannan damuwa, domin lafiyar ki ita ce alfaharin ki wajen mijin ki.
To maganin wadannan cututtuka da kuma yadda za’a hada su, sune kamar haka :
Zaki sami ganyen magarya, ki wanke shi ki sashi a tukunya cike da ruwa, ki tafasa shi sosai, sai ki dauko shi daga kan wutar a barshi shi ya huce.
Sai kina wanke farjinki dashi, sannan ki dan debi kadan kina sha, sannan zaki iya samun roba mai fadi ki zuba shi a ciki kina shiga cikin robar tsawon minti 30. Haka zalika a samu man zogale a dinga sha kamar cokali biyu da rana, biyu da daddare.
Allah yasa mu dace.