Idan ana maganar sanyi, ba ana magana ne kawai akan mura, tari, atishawa, ko kuma ciwon kafa ba kawai. A’a, shi sanyi wani shu’umin ciwo ne wanda yake haddasa cututtuka kala kala, tun daga amosani har zuwa kuraje da dai sauransu.
Ciwon sanyi yana illatar da mata sosai da sosai ta hanyoyi masu tarin yawan gaske, musamman bangaren daya shafi ni’imar dake tattare dasu, da makamantan haka.
Anan zamu kawo muku abubuwan da za’a nema domin hada wannan magani kamar haka :
– A samu Albasa Babba
– Tafarnuwa
– Danyar citta.
Yadda za’a hada :
A yayyanka kanana kanana a samu roba mai murfi ko kwano wanda iska bazata iya shiga ba sai a zubasu a ciki, sannan a samu tafashasshen ruwa azuba a robar, sai a barshi har na tsahon awanni 24, ma’ana kwana 1 kenan.
Yadda ake sha :
Ana shan rabin kofi da safe kafin a karya, sai kuma rabin kofi da daddare kafin a kwanta bacci
Haka zalika wannan hadin yana taimakawa wajen rage kitse ga masu kiba, yana taimakawa a wajen karawa jiki lafiya da kuzari.
Allah ya bamu dauwamamiyar lafiya, Ameen.