1 Akwai nonon daya kwanta akeso su tashi su tsaya char.

2 Akwai kanana anaso su kara girma.
3 Akwai kuma waɗanda girma sukayi da yawa anaso arage su.

Kuma yanzu zanyi miki bayani akan tsayuwar nono da kuma girmansa.

MENENE YAKESA NONO YA KWANTA?

1 Akwai yawan tsalle.
2 Akwai yawan kamasu.
3 Wani kuma nonon haka yake yanada tsayi dama dole yayi
saurin kwanciya.
4 Akwai kuma shekaru.

MENENE YAKESA NONO SU ZAMA KANANA?

1 Akwa halitta wata dama haka Allah yayita nononta kanana ne.
2 Akwai kwanciya akansu
3 Akwai daurin kirji da zani
4 Akwai saka matsttsiyar rigarsa (breziya).

YAYA ZA AYI A GYARA?

Idan nononki kananane Kisamu cukwi Wanda yawansa zai kai guda uku saiki samu garin alkama gwangwani daya, sai aya itama gwmgwani daya, saiki dakasu zasu zama gari ki tankade ki samu nonon saniya idan kuma bakyashan nonon saniya ki samu madara peak ki zuba wannan garin kamar cokali uku (3) ki dama kinasha kullum sau ɗaya (1) sannan ki lura lokacin da zakiyi wanka ki tafasa ruwa da garin hulba aciki kibari yayi sanyi, saiki wanke nonon dashi sannan kiyi wanka.

Wannan hadin matar aure wanda tayi yaye zatayi sannan budurwa itama zata iyayi.

Idan kuma kwanciya sukayi kinaso su tsaya ki kwaba hulba da ruwan dumi,wato garin hulba yadanyi kauri kar yayi ruwa sosai,saikin tabbatar kin gama abunda zakiyi, kinzo kwanciya,saiki shafa,ki kawo brezia damammiya kisaka da safe saiki wanke da ruwan ɗumi, shima wannan matar aure zata iyayi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *