Kasantuwar sanyi yana da illa sosai musamman a jiki da kuma lafiyar mata, hakan yana da matuƙar tasiri ta hanyoyi da dama, da kuma mabanbanta.

Hakan tasa muka ga ya dace mu wayar wa mutane dakai game da hanyar da zasu bi wajen magance matsalar su.

Mata da yawa suna ƙorafi akan, ko kuma sakamakon fitar ruwa ta gaban su, wanda wasu lokutan yana zuwa da wari sosai, duk da yake babu zafi lokacin da yake fita. Amma kuma alama ce daga cikin alamun sanyin mara, wanda akasari ya fiya bayyana a garesu.

To, ga duk macen da take son magance wannan damuwa, sai ta nemo abubuwa kamar haka;

Saiwar zogale
Saiwar kanunfari
Garin kistul hindi
Tafarnuwa

Yadda ake wannan haɗin shine:

Zaki samu tafarnuwa mai kyau ki jajjaga sai ki hadashi da sauran kayan hadin ki tafasa sai ki tace ruwan ki dunga sha, in sha Allah zai tsaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *