Wani abu da yawanmu maza bamu gane ba shi ne yawan lokacin da ya kamata kayi akan matarka a yayi gudanar da ibadar aure. Duk da yake babu …
Duk da yake babu wani bincike daya tabbatar da hakikanin tsawon lokacin da magidanci zai tsawaita akan matarsa, ma’ana yana ibadar aure da ita, sai dai kuma binciken ya tabbatar da cewa:
mafi karancin lokacin da namiji zaiyi akan matar shi shine daga
mintuna 3 zuwa 7, duk namijin da ya kasa daukar wannan lokacin, yana saduwa da matarsa to tabbas yanada matsalar
daya kamata yaga likita.
Haka zalika mintuna 7 zuwa 13 sune yawan tsawon da idan
namiji yayi a lokacin saduwa bai takurawa matarsaba shi ma
baj jigata kansa ba, kamar yadda bincike ya nuna.
Kamar yadda nazarin ya kara tabbatar da cewa, mintuna 10 zuwa 30 akan mace ana amfani da ita, lokuta ne da suka wuce hankali, ga maza masu irin wannan jimawan akan matansu.
Sai dai wadannan tsawon lokatan basu hada da lokutan wasannin motsa sha’awa ba, ana lissafin lokutan ne daga lokacin da shi
maigida ya shigar da azzakarin mashigar.
Babban abunda ya kamata maza magidanta su kuma fahimta anan shine, ba wai ana nufin cewa dole ne sai maza sun dauki
tsawon wadannan lokutan akan matansu ba, ko kuma su
takaita kamar yadda kamar yadda binciken ya nuna ba, abun da
ya kamata maza su fahinta shine ana bukatar kowani
magidanci ya iya fahimtar tsawon lokacin da matarsa take iya
samu gamsuwa a jima’ince.
Akwai wasu matan a cikin mintuna biyu kacal sun biya bukata,
akwai matan da a lokutan wasannin motsa sha’awa ma sun
kawo, kamar yadda ake samun wasu matan muddin ba an
dauki sama da sa’a guda ko rabin sa’a ana gurzarsu ba
basusan ma anayi ba.
Masana sun bada shawaran cewa, ko wani magidanci dole ne
ya fahimci matarsa sosai a jima’ince ta haka ne kawai zai iya
gamsar da ita na babu cuta babu cutarwa. Ganin shi gamsar da
mace a yayin jima’i dole ne akan dukkannin wani magidanci
Ga mazan da suke yin shaye shaye kamin suyi jima’i suna iya
fuskantar Matsalolin ko dai a kamin tsufan su ko bayan tsufan
su.
Ita mace ba wai tsawon lokacin da aka dauka akanta shine ke
sata gamsuwa ba. Kawai magidanci yayi kokarin gano
abubuwan da suke saurin da sauƙin gamsar da matarsa.
Wasa da ita ne ko kuma saduwa da ita ke sata gamsuwa da
wuri. A saduwa da ita dinma a wani yanayin kwanciyar jima’i
take samun gamsuwa. Waɗanan sune abubuwan da maigida
zai gano amma bawai sai yayi shaye shaye ba domin gamsar
da matarsa.
Sai dai babu laifi lokaci zuwa lokaci namiji ya sha maganin da
zai kara masa lafiya gaba ko karin Kuzari, amma kada kuma ya
zame masa idan bai sha wani abun da ya saba sha ba bazai
iya gamsar da matarsa ba