Hanyar Da Macen Dake Son Kugunta Ya Girma Ya Karu Sosai Zatabi.

Bisa fahimta ta mutane da dama, an ta’amlu da girman kugun mace da bada sha’awa ga dukkan lafiyayyen namiji. Dukkan mutum wanda yake daga jinsin maza yanason macen da zata kasance mallakinsa ta zama tana da manyan mazaune, domin suna tabbatar da cikar ni’imar ta.

Ina son a fahimci cewa girman kugu halitta ce, wasu matan har kauce hanya suke yi, suje a saka musu kugun roba. Kun ga akwai alamar kauce hanya anan kenan.

Akwai nau’in ababen da mace za ta rika ci, sannu a hankali, kyan diri da halittarta za su kara fitowa, ita ma za ta rika ji ta kara cika, ta yi kyau.

Masana a wannan fannin, sun bayar da shawarwarin amfani da.

Abarba, Ayaba, Gwanda, Kankana, Zuma da kuma Madara (ta ruwa).

A kan hada su waje guda, a markada su, har sai sun zama ruwa, sai a dan kara zuma da madara. Bayan wannan, mace zata rika sha a koda yaushe. Haka kuma kina iya samun Zogale dafaffe, ki hada da ganyen Alayahu, ki zuba Tumatiri da Albasa, ki yi kwadonsu, ki rika ci.

Haka nan za ki rika yin wadannan kayan lambun da ki ka markada, sai ki rika sha misali da asuba ko da sassafe kafin ki fara cin komai.

Zamu takaita bayanin namu anan, dai mun hadu a karo na gaba da yardar Allah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *