Ba mata kadai bane suke jin zafi ko ciwo a lokacinda ake
saduwa dasu ba. Mazama sunada wannan matsala na cin zafi,
fitan jini a lokacinda suke Jima’i da matansu.
Sai dai wannan ba wata matsala bane da zai tayarwa mai irin
wannan ciwon Hankali. A duk lokacinda namiji ya samu kansa
a hakan, yana da kyau yayi maza ya tuntubi likita.
Sai dai ga wasu dalilai da suke jawo maza suna jin zafi idan
suna Jima’i. Matsalolin sun hada da:
1: Cutukan Jima’i: Irin cutukan da aka dauka a sanadiyan
Jima’i irinsu cuwon sanyi suna iya haifar da jin zafi ga maza a
lokacin Jima’i.
Herpes da cutar gonorrhea suna kumbura gaban namiji, su fito
da kuraje ga kaikaiyi. Wannan yasa namiji idan zai sadu da
mace yake jin ciwo.
2: Loba: Ga mazan da ba a musu kaciya suna iya fuskantar
abunda ake kira a turance phimosis.
Shi wannan matsala yana zuwa ne a lokacinda namiji yayi
kokarin taye fatar lobarsa domin fito da kan kaciyarsa. Idan
fatar wajen a manne yake hakan zai sa shi fitar da jini.
Gabansa ya kumbura yadda idan yana Jima’i dole yaji zafi.
Hanya mafi sauki na magance wannan matsalar shine kaciya a
yanke masa fatar lobar.
3: Matsalar Mafitsara: Idan aka samu matsala a mafitsaran
namiji kamar yadda likitoci suka ce, yana haifar da wani ciwo
da suke kira hypospadias, hakan zai iya jawo namiji ya rika jin
zafi a lokacin Jima’i.
Suka kara da cewa wannan ciwon kuma yana baiwa wasu
kwayoyin cutukan damar shigan namiji da zai kara tsananta
cutar idan ba a gaugauta zuwa wajen likita ba.
4: Cutan Daji: Akwai cutukan daji da suke addaban gaban
namiji wato Penis cancer. Irin wadannan cutukan idan suka
kama namiji gabansa zai kumbura ya kara girma yadda zai rika
masa ciwo a duk lokacinda ya sadu da mace.
5:Priapism: Shi wannan ciwon yakan hana gaban namiji
mikewa, idan ma ya mike bai jimawa zai sake kwanciya. A
lokacinda ya mike zai rika yiwa namiji zafi ba tare da ma ya
sadu da mace ba.
6: Sakamakon Wani Abun: Wasu matan suna cusa wasu
magunguna a gabansu. Wanda wadannan magungunan idan
namiji ya sadu dasu idan bai karbeshi jikinsa ba wato Allergy,
zai iya jawo masa lahani na kuraje ko kaikaiyi a kan
azzakarinsa. Yadda daga bisani zai sa yana jin zafi idan yana
saduwa da mace.
7: Yawan Jima’i: Idan namiji ya takurawa kansa da Jima’i fatar
gabansa yana iya dayewa, musamman idan matarsa batada
ni’ima sosai. Haka zai haifar masa da ciwon da idan yaso
saduwa da mace zai rika jin zafi. Hypersensitivity.
8:Ciwon Fata: Cutukan fata irinsu Zoon’s balanitis, erosive
lichen planus, lichen sclerosis, a cewar likitoci suna iya
jawowa namiji ciwo akan gabansa. Hakan kuma zai iya sashi
jin zafi Idan yana saduwa da madam.
Kada kaji kunyar tinkaran likitanka idan har kana fuskantar
daya daga cikin wadannan cutukan dake sa jin zafi idan ana
Jima’i. Ka tabbatar ka kauracewa sadu da iyalinka da zaran ka
fahimci hakan. Domin ciwon naka zai iya shafarta.
Ka tabbatar dacewa ka ga kwararren likita ne ba wanda zai je
ya baka maganin da zai kashe maka azzakari ba.