SINADARIN YALWAR GASHI
duk macen da take son gashinta yayi yawa, kuma Yayi tsawo ya dinga sheki sai ki samo wadannan maya-mayan da Zan fadi
– Man habbatussauda
– Man zaitun
– Man kwakwa
ki dinga shafa su a kowane lokacin
SINADARIN HANA ZUBEWAR GASHI
Duk matar da take son kar gashinta ya zube kuma taga yana Kara tsaho to ga dama ta samu, sai a samo wadannan maya-mayan da za a fada ta dinfa shafa su sune:
– Man gelo
– Man basilen
SINADARIN SAMUN RUWAN NONO
yar’uwa duk macen da take da karancin ruwan nono, to ga hadin da Zaki yi yar’uwa, za ki sami ruwan nono mai yawa, ga mahadan da Zaki tanada ki dinga sha aka-akai sune:
– Madara ( peak)
– Garin gero
– Zuma
MAGANIN CIWON NONO
Maganin ciwon nono ya kasu kashi daban-daban amma ga kaso daya daga cikin su, duk macen da take fama da ciwon nono da kuma rashin ruwa to sai ta sami garin hulba da garafin ta kwaba su da ruwan dumi, ta shafa tayi haka kamar sau uku, ( 3 ) ma’ana wuni uku Allah yasa mu dace.
MAGANIN CIWON MARA
Ciwon mara wani abune da yake yawan damun ya’ya mata musamman a lokacin al’ada, to shi yasa na kawo maganin wannan matsala a cikin wannan post duk lokacin da kika fara jin ciwon ciki, sai ki sami:
– Zuma
– Zaitun
sai kowan ne ki sha babban cokali ( 2 ) da safe da yamma
*MACEN DA TA SAMU BUDEWAR GABA*
duk matar da gabanta ya bude amma ba ta San yarda zatayi ya koma ba, taba dama ta sami yar’uwa ita dai wannan hanya tana da yawa, amma ga wata hanya da Zaki Bi mafi sauki itace:
ki samo wadannan mahadan da Zan fadi.
ki tafasa shi ,ki matsa lemon tsami dan kadan a ciki, ki dinga zama, zai hade ya koma dai-dai
sassaken bagaruwa
MAGANIN RAGE GIRMAN NONO
Mace da Allah yayi mata wannan baiwar kuma take jin yana damunta kuma take son ya rage girma, sai ki samo MUSDAKKIRIN ki shafawa nonuwa insha Allah zasu rage girma
DOMIN SA GIRMAN NONO
macen da take son nonuwanta su Kara girma to ga dama ta samu, domin da yawa zaka ga mata, suna da sha’awar haka, to ga hanya mai sauki
– Cukwui
– Gero
– Alkama
– Citta
– Nasoro
sai ki dake su gaba daya a guri daya, sai ki samo madara mai kyau sai ki ringa debo wannan garin kina zubawa a madarar kina sha Zaki ga abin mamaki.