A nemi dabino busashe a cire kwallon sai a nike, sai a nemi ‘ya’yan magarya wadanda suka bushe sosai, suma cire kwallon sai a dake, duka za’a maida su gari, sai a zanka sanya cokali karami na kowanensu guda biyu sai a yi shayin nasu a cikin karamin cup na ruwan zafi ba sugar ba madara,ba zuma,ba Lipton,da safe a sha ko a duk sanda aka ci abinci za’a iya sha ko a sanda ake bukata.

1. Karin basira da lafiyar kwakwalwa.

2. Sinadirran vitamins ne masu Karin kuzari da lafiya ga jiki.

3. Yana Karin yawan ruwan maniyi ga namiji

4. Karin karfin jiyoji da kasusuwan jiki

5. Yana taimakawa mata masu juna biyu dake yawan laulayin ciki.

6. Yana magance barazanar kamuwa da cutukan daji.

7. Maganin zafin jiki da kumburin ciki

8. Maganin hauhawan jini

9. Maganin rashin samun isashen bacci,ka konta jiki yayi tayima ciwo bacci yazo ya gagareka.

10. Yana karawa ciki lafiya.

11. Sinadirran vitamin C ne natural masu kyau da karfi.

12. Maganin tarin asma

13. Yana tsayarda gudawa ga mace ko namiji

14. Yana karawa idanu lafiya

15. Mace mai shayarwa zata iya sha yana kara ruwan mamma masu rai masu lafiya.

Allah yasa mu dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *