Ana gyaran fuska ne domin ta kasance babu wani tabo ko kurji a jikin ta, domin haka muka kawo muku hanya mafi sauki da zaku bi wajen tabbatar da fuskar ku tayi haske sosai.

Alfanun ruwan kwai a jikin fatar Dan Adam sun hada da :

1- Ruwan kwai nada sinadarin gina jiki, da kuma sinadaran Bitamin.

2- Ruwan kwai na rage tsufar fuska Danyen ƙwai.

3- Danyen kwai na kare fuska daga yawaitan fitar kuraje.

4- Danyen kwai na kara ma fuska haske.

5- Ruwan kai na rage kumburin idanu Yadda ake hada ruwan kwai don samun bukata shine, za’a fara turara fuska da ruwan zafi, sa’annan abi da Rose water a shafe fuskar, kamar yadda majiyar mu ta ruwaito.

Daga nan sai a fasa kwai, a cire kwaiduwar, sai a kada farin ruwan kwan, har sai yayi kumfa, bayan nan sai a shafe fuska da wannan ruwan kwai, sai kuma a daure fuskar da takardar ‘Tissue’ a manna a fuskar, a kara samun takardar a sake mannawa a dukkanin fuskar.

Da zarar fuskar ta bushe a haka, sai wanke fuskar, sa’annan a shafe fuskar da kwaiduwar ita ma, sa’annan a wanke, idan an cigaba da wannan tsari, za’a samu biyan bukata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *