Wannan hadin yana gyara fuska tayi sumul babu tabo ko daya a jikinta, sannan fuska za tayi haske sosai, ta yadda kurajen fuska zasu fita. Sakamakon kowanne mutum da yadda yake tafiyar da rayuwarsa, da kuma kula da tsabtar jikinsa, wannan hadi zai taimaka wajen fitar da dukkan kuraje da kuma tabo a fuska.

Don kasancewa cikin kyawun fuska da kuma fatar jiki, sai a nemi abubuwa kamar haka :

– Tumaturi
– Madara peak

Bayanin Yadda Za’a Hada ;

Zaki hade su guri guda ki kwaba dai-dai gwargwadon yadda zai isheki sai ki shafa a fuska ya samu tsayin mintuna talatin akan fuskar taki sai ki wanke, wannan yana gyara fuska sosai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *