Kiba wata halitta ce da take zama nakasu ga wasu mutanen ta bangarori da dama, musamman wadanda suke fama da ciwon sugar, da kuma ciwon sarkewar numfashi, da dai makamantan su.

Wasu mutanen basa son kiba ne sakamakon halin da take jefa su, na rashin sakewa a cikin al’umma, da sauran abubuwa da suke gani abin kyama ne a tattare da ita. Don haka, duk wanda yake son rage kiba ta hanyar da ba za’a cutu ba, to sai yayi amfani da wannan hadi.

Abubuwan da za’a nema :

– Lemun tsami 1
– Zuma cokali 3
– Citta danya guda 1
– Ruwa 50cl

Yadda Za’a Hada :

Ki wanke lemunan duka seki yanka ki rabasu hudu, amma ba sekin cire bawon ba seki zuba ruwan, ki gurza citta ki zuba ki kawo zuma kisa, seki dora awuta kisa wutar kadan, harse ya dahu seki sauke, ki bari ya sha iska seki muttsuke ki tace kisha. Yana rage qiba sosai in sha ALLAHU, idan kuma kinaso kiyi da yawa ne to saiki sa komai kaman yanda na fada sannan ki dura a jarkoki sannan ki saka a fridge kullum kisha safe da kuma dare (Maza ma suna iya amfani dashi).

Allah yasa mu dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *