Idan kaji ance wane ko kuma wance, to ba banza ba, musamman a al’amari daya danganci sirrin maigida da uwargida. Rashin kasancewa ko kuma amsa sunanka a matsayin namiji lokacin da kake raya sunnah abu ne mai matukar sanyaya gwiwwar ko wane magidanci.

A lokacin da maigida ya kasa tagaza komai wajen tabbatar da biyawa matarsa bukatarta ta Aure, hakan ba karamin nakasu yake zama a garesu ba, don matan nasu suna iya kiran su da ragwage, ko kuma suna makamancin haka da yake nuna alamar rashin juriya.

Wasu lokutan rashin kwarin azzakari ko kuma girman sa ne yake jawo al’amari irin wannan. Don haka ya rage ga mai shiga rijiya, kodai ka nemawa kanka magani domin ka farantawa kanka da kuma iyalin ka, ko kuma la shiga hakkin ka da kuma nasu.

Domin sanin sauran kayan da za’a nema wajen hada wannan magani, zamu kawo muku su kamar haka:

– Madarar ruwa ko gari.
– Man kustulhindi gari.
– Citta ta gari ko ruwan.
– Zuma

Hanyar da za’a hada shine:

A samu Madarar mai kyau yar waje ko peak milk da sauran madara dai mai kyau, za’a tsiyaya ruwan chitta ko garin citta daidai misali. Sai a samu garin Kustul Hindi cokali daya a zuba aciki, daga nan se a sanya zuma daidai Misali se a shanye hadin duka, Minti 30 kafin kwanciya.

Da yardar Allah za’a samu biyan bukata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *