Kaɗan daga cikin amfanin itacen Kalgo
Wannan itacen yanada amfani tafuskar wasu magungunan gargajiya.
Musamman yayan sa sunada matukar taasiri sosai akan magance, wasu matsalolin abangaren kiwon lafiya.
Idan kasamo yayan kalgo kawanke suka bushe ,kayi garin sa ko karika shansa da ruwa zalla, ko kuma kowanne nauin abin sha insha Allah, yana taimakawa wajen saukaka matsalolin da suka shafi ciki, da mara, kashi, jijiya, bargo,musamman idan zaka sha da no-no abangaren cutuka wadanda suka shafi jini, da kuma ruwan jiki.
Kuma kada kararrabe wasu daban gaba daya jimla matsalolin daban daban, amma ana tabbatar da aikin magani ne alokacin da
aka jarraba.
Garin yayan kalgo idan mata sukayi amfani dashi yana taimakawa wajen basu Niima.
Yana saukaka ciwan suga.
Yana kara lafiyar namiji idan aka haɗa shi da lemun tsami, citta,kaninfari, tafarnuwa, masoro.da zuma.
Bayan haka idan kanaso dabbobin suzama da lafiya kuma suyi bulbul samo shi karika hadawa da dussa kabasu sunaci kayi kallon ikon Allah.
Wannan zaka iya jarraba shi akan kowacce cuta ne Kamar yadda nafada asama insha Allah. Amma akwai itatuwa Kala biyar duk da wannan wadanda ake amfani dasu akan cutuka daban daban, insha Allah.
Dafatan Allah taala yabamu dacewa Allahumma Ameen.