Mata da yawa suna korafin jin zafi a lokacin da ake jima’i dasu sakamakon wadansu al’amura da suke faruwa a jikinsu, na matsalar sinadarin halitta na “hormones”, haka nan abin yana sanya su tsoron yin jima’i da mazajen su.
Jin zafi lokacin jima’i abu ne da yake buƙatar ayi bayani akan sa, domin yana sanya mata da yawa tsoro da kuma fargaba. Hakan har yana jawowa mace taji gaba ɗaya bata sha’awar saduwar aure da mijin ta bisa dalili ko kuma saboda idan har tayi jima’i zafin nan shi zataji.
Amma kasantuwar kowanne irin yanayi mutum yake ji, babu wata fa’ida a zauna ba tare da an nemi magani ba. Shafin MISMOB yayi sannan kuma yanayin iyakar ƙoƙarin sa wajen ganin sun binciko hanyar da mace zata samu maganin jin wannan zafi yayin jima’i.
Domin haɗa wannan magani, za’a nemi kayan haɗi kamar haka :
– Hatsi wanda aka surfa
– Kayan kamshi
– Kanunfari
– Man shanu
– Mazarkwaila
Bayani Gameda Yadda Zaki Haɗa ;
Zaki nemi dukkan kayan haɗin da aka ambata, sai ki tafasa su a cikin tukunya wuri guda ɗaya sai ki tace ki zuba shi a cikin abin adanawa mai kyau a riƙa sha.
InshaAllahu za’a samu biyan buƙata.