Idan muka ce gyaran nono akasari ba kowace mace zata gane me muke nufi ba saboda basu damu da gyarawa ba, alhali kuma rashin gyaran ba karamar illa yake yi musu ba amma su basu san hakan ba.

To gaskiya yana da matukar muhimmanci da tasiri ga mace AMARYA ko UWARGIDA, BUDURWA KO ZAWARA, da ku gyara nononku, karki bar nononki hakanan sharaf ba kyan gani.

Abin mamakin ma sai kaga mace ta bar nono a zube, in tana shara mai gida yaga suna ta reto kamar an ratayo agwagi a bayan keke, idan kuka lura sai kuga matan wadansu kabilu wadanda ba hausawa ba (kamar LARABAWA KO TURAWA) sun tsufa ko sun manyanta amma martabar nonuwansu sunanan daram, ta yadda ko nonuwan wata budurwar a nan baza ka samesu a haka ba.

Hakan zai iya rage miki tasiri wajen maigida, hanyoyin da zaki bi don kada nononki su fadi, ko kuma idan ya fadi kuma kina so su tashi, sai a samu abubuwa kamar haka :

1. Alkama ki rinka yin kunu da ita kina sha safe da rana
2. Garin hulba
3. Garin tsamiya
4. Zuma farar saka
5. Lemun tsami

Sai ki hadasu guri 1 ki rinka shafawa a nonon, bayan awa
daya ko ( 30 minutes) sai ki wanke ki shafa man zaitun,
malama zaki sha mamaki.

GYARAN NONO GA BUDURWA

Wannan wani hadi ne da akeyi don gyaran nono musamman ga budurwa, shi wannan hadi kuma kowace macema intana bukata zata iya amfani dashi saboda tasirinshi, yanda akeyi shine za a samu.

– Garin waken soya
– Garin alkama
– Garin zogale
– Garin bawon lemun zaki
– Kunfan maliya
– Zuma

Saiki hada su guri daya, ki rinka shafawa a nonon bayan minti 30, ko sama da haka. Sai ki wanke, sannan kuma ki rinka shan kunun alkama zaki sha mamaki.

DON DAWO DA MARTABAR NONO DA GIRMANSA

Ga matar da take son ta dawo da martabar nononta ko girmansa yanda zatayi shine zata samu,

– Ganyen sabara mai kyau
– ‘Ya’yan alkama suma masu kyau
Sai ki rinka kunu dasu, ko kunun gyada, ko kunun alkama, ko kunun shinkafa, ko kunun gero, ko kuma duk dai wanda yasamu sai ki dafashi da wannan hadin mai albarka.

Allah yasa mu dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *