Jama’a ga wani hadi da ba kowa ya san da shi ba,amma kuma maganine mai dadi mai karfi,a jarraba a ga abun mamaki.

Duk Wanda ya amfana yayi man addua Allah ya cikamin burina na alhairi.

– Bushewar ciki,ka nemi citta danya yar qarama haka ,da rake babba guda biyu,bayan kaci abinci kantamna cittar sannan ka sha rake.

– Shawara : Ka tamna citta qwara daya sannan ka sha rake bayan ka karya da safe,a fake yin haka kullum zuwa wata daya zaka ga yanda zaka rinka yin fitsarin shawara.

– Tsananin gajiya da kasala : Ka nemi rake ka zanka sha bayan ka yi aiki ko a sanda kake jin gajiya.

– Karfin jiki : Ka sha rake a kullum bayan kaci abinci.

– Karamcin ruwan jiki : A kullum ka sha rake safe,rana da yamma bayan kaci abinci

– Zafin ciki : Ka tafasa rake da citta qwara daya ka zanka sha kamun ka konta bacci da sanda ka tashi bacci.

– Taurin bahaya na basir ka zanka shan rake akai akai.

– Tarin majina da asma ka tafasa rake da citta ka sha cup da safe daya,ka sha a kullum, zaka ga yanda zaka rinka fitarda matacciyar majina daga huhunka.

– Ciwon ciki mai murdawa ka nemi citta da rake kayi blending ka sha cup daya bayan ka karya.

– Kumburin ciki : Idan ka ci wani abu da ya kumburuma ciki to ka nemi rake ka sha bayan wasu mintuna zaka ji wasai.

– Zafin jiki : Jikinka na zafi haka kawai ka fake shan rake kullum da safe kamun kaci komai.

– Guba : Idan kaci wani abu da kake ganin zai iya 6ata ma ciki to ka nemi rake da citta ka tafasa ka sha.

– Rama da bushewar jiki : Ka zanka zuba ruwan rake a cikin koko kana sha.

– Karamcin ruwan maniyi : Ka nemi garin aya ka dama da ruwan rake kana sha zaka ga abun mamaki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *