Akwai mutane da dama wadanda suke fama da matsalar kawowa, ma’ana mutum daya fara saduwa da mace ba zai dauki dogon lokaci ba, sai ya kawo ba tare da ita macen ta gamsu ba, wanda hakan ba karamin shiga hakkin matar ake ba.

A bisa wannan dalili, shafin “Mismob” suka yi muku wannan kyakkyawan tanadi akan matsalar data shafi saurin kawowa a lokacin saduwa da iyali.

Abubuwan da ake bukata yayin hada wadannan :

1. Cucumba ko Gurji

2. Zuma

3. Madara

Yadda ake wannan hadi :

Za’a markada cucumber ba tare da an kankare ko fere ba, sai a zuba zuma da madara a ciki, sannan haka za’a rika sha har tsawon sati daya zuwa biyu.
Idan ya kare sai a sake wani hadin.

Za’a iya sakawa a cikin firji (fridge), domin yin sanyi saboda kada hadin yayi saurin lalacewa.

Allah yasa mu dace. Ameen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *