Tsamiya na daya daga cikin ‘ya’yan itatuwan da ake amfani dasu a kasar Hausa kama daga fannin abinci da kuma magani .
Tana da amfani mai tarin yawa haka kuma tana da wasu illoli musamman idan aka sha ba’a bisa ka’ida ba,tana kuma da illa ga wasu daidaikun mutane,domin akoi mutanen da take tadoma cutukkan iska kamar na kumburi ko qaiqayi da kurajen jiki.
Ana amfani da tsamiya wajen sarrafa kayan sha,inda a yau wajaje dadama wasu kan qullata a leda bayan sun tace sun gaurayata da sukari sai su sakata a na’urar sanyi (refrigegrator).
Wasu kuma sun dauketa a matsayin magani ko a hada abinci da ita domin akan yi kunun tsamiya da kuma tuwon tsamiya a wasu yankuna kamar a Zuru,ri6a da suru dake a jihar kebbi.
Shafin kula da lafiya ya gano matsalolin da tsamiya ke magancewa.Ga kadan daga cikinnsu :
1.Cushewar ciki da rashin yin bahaya.
2.Ciwon ciki.
3.Tashin zucya ga masu juna biyu.
4Tsutsar ciki.
5.Matsalolin da suka shafi na hanta (liver da kuma madaciya (bile)
6.mura da zazza6i.
7.Tana wanke dattin ciki da kuma cushewar hanji
8.Ana amfani da ganyenta wajen magance cutukkan daji (cancers)
9.Ana tafasa ruwanta ayi wanka dasu dan magance ciwon ga6o6in jiki.(arthriries)
10.Tana saka cin abinci,a duk sanda ka ci abinci ka sha tsamiya to za kayi saurin jin yunwa.
Illolinta sun hada da :
Tsamiya tana iya haifarda illa ga masu ciwon sukari (diabeties patients) saboda tana illa ga adadin yawan sukarin dake a cikin jini.
Haka kuma ga wadanda za a yiwa fida (surgery) to kada su sha tsamiya a kalla makonni biyu kamin ayi tiyata.
Gamai fama da rama,yawan shan tsamiya na iya kara sanya ramar saboda tana rage qiba sosai.
A guji shan tsamiya a sanda ake shan
wasu magunna rukunin Ibumol da aspirin.
Tsamiya tana rage shawar namiji,idan matsananciyar shawa ta yiwa namiji yawa to ya lazimci shan tsamiya zaiji leqes.
Idan kiba ta yiwa mutum yawa a jiki kuma yana son ya rage kibar to ya zanka shan tsamiya amma a san adadin da za a sha.
Mai fama da gembon ciki ya san yanda zaiyi ta’ammali da tsamiya.
Allah yakara muna lafiya