1. A kula da tsafta: Rashin tsafta na ƙara yiwuwar samun wasu sabbin cututtukan wanda hakan na iya yaɗa su ga makusantan mutum.

2. A dinga amfani da BAYI (toilet) mai tsafta sabida gujewa sake kamuwa da shi cutar sanyin (infection).

Domin samun gogayya da ruwa ko abubuwan da infection ɗin ya manne masu na iya dawo da shi Cutar sanyin, hasali ma har da ƙara ma mutum sababbi.

3. A dinga sa ɗan kamfai (pant) na auduga (cotton). Domin ɗan kamfai na roba/leda (nylon) na taimakawa wajen bunkasa samuwar yeast infection.

4. A kammala shan magani koda dukkan alamun sauƙi sun tabbata. Wannan na da mahimmanci domin rashin shanye dukkan magungunan na iya sanya mutum cikin haɗarin ƙara samun ciwon na sanyi wanda kuma ba zai ji magani ba ma.

5. A wanke hannu sosai yayin da za’a sa maganin nan da ake cusa wa cikin farji, hakazalika in za’a shafa na shafawa a wajen.

Hakan na da mutukar mahimmanci domin rage yiwuwar gurɓata maganin ko cusa wasu kwayoyin halitta masu iya cutarwa. Haka kuma a wanke hannu yayin da aka gama.

Sunana Pharmacist Musa A Bello, na damu da lafiyar al’umma, kai ma ka bada gudummawar ka ta hanyar liking da sharing.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *