Barkanmu da sake kasancewa daku a wannan shafin namu mai albarka “Mismob”, da fatan kowa yana lafiya, A yau zamu kawo muku yadda ake gyara hammata. Idan an gyara jiki kada a manta cewa akwai inda yafi muhimmanci da kuma bukatar a kula da shi.

Musamman ma bayan an aske gashin gurin, akwai hanyoyi da za a bi don hana wajen yin wari tare da baki. Abubuwa da dama ne suke kawo hammata tana wari ko kuma tayi baki, koda kuwa an aske gashin dake wurin.

Ga hanyoyin da za’a bi kamar haka :

1. AMFANI DA MAN KWA-KWA:

Babban abin da ake amfani da shi a wajen hada man zamani shi ne man kwa-kwa domin yana dauke ne da sinadarin kara haske kuma yana da vitamin E.

A shafa man kwa-kwa a hammata a kullum a yi minti goma kafin a yi wanka Bayan an yi haka sai a wanke da sabulu mara karfi (wanda sinadaran da akan hada shi ba mai zafi ba ne) da ruwan dumi.

2. AMFANI DA GURJI DA LEMON TSAMI

Kamar yadda aka sani cewa ruwan lemon tsami nasa hasken fata, haka kuma gurji shi ma na dauke da sinadarin kara wa fata haske da kuma sanya ta laushi da sulbi. A hada ruwan lemon tsami da markadaddiyar gurji a guri daya sannan a shafa a hammata. A bari ya jima na tsawon mintuna goma sannan a wanke da ruwan dumi.

3. GARIN KURKUM DA KWAI:

Kurkum ma na dada wa fata haske za’a iya kwaba garin kurkum da ruwan kwai sannan a shafa a hammata bayan mintuna goma zuwa sha biyar sai a wanke da ruwan dumi. A kullum kafin a yi wanka.

4. ASKI

A daina barin hammata da gashi a yi kokarin aske shi a lokacin da ya fito. Domin idan da akwai gashi a hammata, zai hana gumi bushewa zai fara tara shi yayi ta ba da wani irin wari. Sai a ga koda an fesa turare, sai a ji kamshin turaren daban, warin hammata kuma daban.

Yin amfani da wadannan ababen wajen gyaran hammata zai rage warin jiki da kuma hana fesowar kuraje da fitowar bakar kala a karkashin hammata da kuma rage gumin hammata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *