Lemon tsami yana cikin muhimman ƴaƴan itace da likitoci suka ce suna da muhimmanci a jikin ɗan Adam saboda sinadaran da ke ƙunshe a cikinsa.

Akwai nau’in lemon tsami daban-daban a sassan duniya, amma wanda aka fi sani shi ne ƙarami mai tsami musamman a Afirka da yankin Asiya.

Mujallar lafiya ta Healthline a wani cikakken bayani da ta wallafa game da lemon tsami da amfaninsa ta ce lemon tsami yana ɗauke da sinadarin Vitamin C sosai, kusan yana samar da kashi 20 na buƙatar mutum.

Yana kuma ƙunshe da sinadarai na iron da calcium da vitamin B da Potassium da magnesiums.

Binciken ya bayyana cewa ci ko shan lemun tsami yana ƙara ƙarfafa garkuwan jiki, yana kuma rage barazanar kamuwa da ciwon zuciya da kansa da ciwon koda da kuma inganta lafiyar fata.

SHIN LEMON TSAMI NA TSINKA MANIYI ?

Wasu mutane sun dade suna ganin cewa shan lemon tsami yana illa ga rayuwarsu ta aure, inda tsakanin al’umma ko kuma a al’adance ake bayyana cewa lemon tsami yana tsinka maniyin namiji. Wani lokaci ma akan faɗa wa mutum cewa shan lemon tsami yana rage ƙarfin sha’awa ga maza da mata da kuma rage ƙarfin mazakuta.

Sai dai Hajiya Jummai Hassan, wata ƙwararriyar likita kan abinci da ke asibitin Wuce a Abuja, babban birnin Tarayyar Najeriya, ta shaida wa BBC cewa, baya ga amfanin lemon tsami a hanyoyi daban-daban na lafiya yana kuma ƙara inganci da gyara maniyin mutum.

Ta ce lemon tsami yana da amfani da yawa ana – amfani da shi ta hanyoyi daban-daban wurin sha da kuma abinci.

“Yadda mutane suka dauka cewa lemun tsami yana da matsala ga ma’aurata ba haka ba ne domin yana da amfani a jiki sosai. Domin wani bincike ya nuna cewa idan ana shan sa ba da yawa ba yana gyarawa da inganta maniyi.”

“Ɗan ruwan lemun tsamin da ake matsawa a ruwa ko a shayi a sha bai kai yawan da zai tsinka maniyi ba- sai dai ya gyara da inganta shi.”

“Nasan duk yadda ake shan lemun tsami ba a matsa shi har rabin kofi zallarsa a sha – amma ɗan matsawa kadan ba shi da wata matsala ga lafiya ko tsinka maniyi kamar yadda ake cewa,” inji kwararriyar likitar abincin.

Sai dai kuma ƙwararriyar likitar ta ce shan lemun tsami da yawa a lokaci ɗaya yana iya tsinka maniyi musamman ga masu son ƙayyade iyali kamar waɗanda ba su son haihuwa.

Ta ce akwai bincike da aka yi a Australia wanda ya nuna cewa yawan shan Lemun tsami adadi mai yawa a lokaci guda yana iya tsinka maniyi.

“Idan an yi amfani da shi a jiki kafin jima’i ko kuma a matsa ruwansa sosai a sha zai iya tsunka maniyi.”

Shan sa ne da yawa lokaci daya ne ba a so- Kuma duk abin da ya yi yawa yana da matsala amma baya da wata matsala ga ma’aurata
Yadda lemon tsami yake da sinadarai a cikinsa kamar Vitamin C da Potassium da Magnesium. Ana amfani da shi ta hanyoyi daban daban.

Likitoci sun ce ana son mutum idan ya tashi daga bacci ya sha lemon tsami, ya matsa a cikin ruwa a kofi ya sha.

Dakta Jummai ta ce an fi son mutum ya matsa lemon tsami ya sha a ruwa maimakon gahawa domin a cewarta, gawaha na ture sinadaran da ke jikin mutum a fitar a fitsari.

Amma idan lemon tsami aka sha sinadaran za su zauna a jikin mutum da za su yi masa amfani a jiki.

Sannan an fi son mutum ya matsa lemon tsami a ruwan dumi a sha a kullum.

Ba a son mutum ya dinga matsa zallar lemun tsami ya cika kofi yana sha. Amma idan za a dan matsa kadan a sha yana da amfani sosai ga lafiyar jiki.

Lemun tsami ana son a sha da safe da kuma idan za a ci kifi ko a salat a matsa a ciki.

SHIN LEMON TSAMI YANA ILLA GA MUTUM ?

Masana lafiya sun ce duk da amfanin da lemon tsami yake da shi da dama a jikin mutum amma kuma zai iya yi wa wasu illa musamman ga masu ciwon ulsa.

Lemon tsami yana da ɗauke da sinadarin asid sosai kuma Ulsa ciwo ne da ba ya son asid, wanda idan mutum yana da ulsa ya sha za ta iya tashi.

Kwararriyar likitar abinci a asibitrin Wuse Hajiya Jummai ta ce shan lemun tsami ya danganta da lafiyar mutum domin duk abin da yake da amfani ga wani yana kuma iya zama illa ga wani.

Haka kuma akwai mutanen da jikinsu ke zaɓar nau’in abincin da yake so. Wasu za su iya shan lemon tsami ya sa su amai ko kuma zafin zuciya da kumburi, kamar yadda bayanan Mujallar lafiya ta Healthline suka nuna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *