Ana daukan cutar sanyi ne tsakanin macce da namiji, duk wanda keda cutar yana iya likawa wani lokacin saduwa.

Ana iya daukar cutar idan kin saka panties din mai cutar (ga mace) ko gajeren wando (ga namiji) wadanda ke dauke da cutar.

Idan mai cutar taje toilet da buta ta kama ruwa, idan hannun ta ya taba gaban ta sai ta rike butar da wannan hannun sannan ta fito da ita, wata macen kuma ta dauki butan taje tayi amfani da butar har ta taba gaban ta. Itama zata dauka ta wannan hanyar.

Kama ruwa da ruwan dake dauke da wadannan cututtukan ko wanka cikin pool din dake da gurbataccen ruwa.

Akwai hanyõyi da yawa da ake iya daukan wannan cuta ba tare da macce ko namiji sunyi sex ba.

Amma bincike bai tabbatar da ana iya daukan wannan cutar ta hanyar shiga toilet ba kamar yadda mutane da yawa suke fadi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *