1. SHAYAR DA YARO

i Idan mai shayarwa tana so nononta ya wadaci jaririnta kuma kada ciwo ya kama nonon nata sai ta ci dabino bakwai sannan ta sha man tafarnuwa cokali daya.

2. CIWON CIKI DA KULLEWAR MARA

Bayan haihuwa, sai a sami ruwa mai dumi kofi daya a zuba man cikin cokalin shayi daya sai ta sha ta yi haka har tsawon kwana uku.

3 ABINDA YA SHAFI HAILA, FITSARI, DA JININ BIKI

Wanda ke yin bayan gari da kyar ko fitsari da kyar ko wajen fitar jinin haila sai an sha wuya ko jinin biki, sai ta rika shan karamanin cokali daya da safe daya da rana daya da dare, zata warke sai dai budurwar da take da budurcinta idan ta fiya yawan yin amfani da man tafarnuwa zata rasa budurcinta.

4. MUHIMMIYAR FA’IDA

Idan mace tana bukatar maniyyinta ya yawaita sai ta sami madarar saniya kofi daya ta zuba man ta sha kofi daya da safe, kofi daya da dare, matar da tayi haka zata bai wa mijinta sha’awa da mamaki matuka.

5. WACCE TAKE SON FARJINTA YA TSUKE YA ZAMA DAN KARAMI

Matar kuma da take so farjinta ya zama a tsuke dan karami, daidai yadda zata gamsar da mijinta yadda idan ya sadu da ita ba zai sake tunanin wata ba.
Sai ta sami “DEER MUSK ” rabin-rabi na cikin cokalin shayi daya, sai ta hada da cikin cokali daya na man tafarnuwa ta gauraya, sannan sai ta tsoma da auduga mai kyau tasa a gabanta, bayan awa 3 sai ta cire ta yar da audugar tayi haka sau hudu ko sau biyar idan tayi haka gabanta zai dawo daidai da na budurwa wadda wani bai taba kusantarta ba amma a tsuke wa ba budurci ba.

– AMFANIN MAN TAFARNUWA GAME DA MAZA

A wannan babi kuma zan kawo amfanin man tafarnuwa game da maza. Idan namiji yana jin kaikayi a Nikon MARAINANSA ZAKARINSA
to, sai ya sami garin farar kanwa cikin babban cokali daya, ya dafa da ruwa kofi biyu, idan ya tafasa sai ya zuba man tafarnuwa babban cokali biyu ya gauraya sannan ya sauke, idan ya huce sai ya wanke gabansa gaba daya da ruwan zai sami sauki.

1. WANDA BAYA IYA SADUWA DA IYALI

Wanda baya iya saduwa da iyali fiye da sau daya ko kuma da ya soma sai ya ji ya gaji, to sai ya sami dabino mai kyau guda 113 ya dafa da ruwa mai kyau, idan ya tafasa sai ya tace da farko zai dafa da ruwa kamar kofi hudu 4 bayan ya tace sai ya debi kofi uku ya sake tafasawa yana cikin tafasa sai ya zuba man tafarnuwa babban cokali biyu 2 sai ya barshi akan wutar ta yadda ruwan zai dawo kamar kofi biyu 2 idan ruwan ya huce sai ya rika sha babban cokai biyu sau hudu a rana, ya yi kwana 7 yana yin haka…

2. GAME DA GWAIWA KO TINJERE KO KAMAU KO FITAR WANI RUWA DAGA AZZAKARI .

Wani ruwan a kan ganshi da yauki-yauki kuma rawaya-rawaya, wannan ruwa ba ciwon sanyi bane, alamu ne da suke nuna cewa gwaiwa na tafe.
Maganin wadannan abubuwa shi ne a sami zuma mai kyau tatacciya kofi uku (3) a sami man shanu kofi (2) a sami man tafarnuwa cikin babban cokali hudu a hada su guri daya a dafa, su cakuda sannan a sauke, idan sun huce sai a rika sha cikin babban cokali biyu (2) sau hudu a rana.

3. WANDA ZAKARINSA BA YA TASHI SOSAI KO KUMA IDAN ZAI KUSANCI IYALI SAI YA KWANTA

Amma kada ka manta akwai na aljanu idan ka gwada wanna sai ka nemi malamai
ya samu garin kanimfari cikin babban cokali biyu, ya sami wani abu da ake kira da turanci ” TEMPLE INSENCE ” ya dake ya debi cikin cokali (3) sai ya sami madarar saniya kofi biyu (2) ya zuba man tafarnuwa babban cokali hudu (4) ya gauraya sai ya sha rabin kofi da RANA DA YAMMA RABI DA DARE RABI DA SAFE idan ya yi haka sai yayi fashin kwana daya, sannan ya sake yin haka sau hudu (4).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *