Kamar yadda kowacce cuta a fadin wannan duniya take da magani, haka zalika kowanne abu a duniya yana da nasa amfanin, watakila ta hanyar waraka ko kuma ta wata hanyar daban.

Garin hulba shima yana da nasa amfanin, musamman wajen mata wadanda suke dauke da juna biyu (ciki). Amfani dashi yana taimakawa sosai wajen rage ciwon mara na mata, da kuma karin lafiya a jikinsu.

Don haka duk macen da take fama da ciwon mara musamman mai dauke da juna biyu (ciki) to ga hanyar da zata bi domin ganin ta magance wannan matsalar.

Zaki nemi kayan hadi kamar haka;

– Garin hulba
– Garin habbatus sauda
– Zuma

Yadda Zaki Hada:

Zaki samu wadannan kayan hadin sai ki hadesu guri guda ki tafasa ki tace ruwan ki zuba Zuma ki dunga sha, in sha Allah zai daina ciwo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *