Idan har maigida yana da dama da matsala wajen karfin gaba, ma’ana karfin mazakuta wanda hakan ke zama nakasu a gareshi wajen kwanciya jima’i da iyalinsa, da kuma biya musu bukatar su kamar yadda suke so.
To abinda ya kamata shine a nemi wadannan abubuwan kamar haka :
– Garin habbatus-sauda cokali 1
– Kwai guda biyu/uku
YADDA ZAKI HADA MASA :
Ana so kina zuba garin habbatus-sauda a cikin ruwan kwai, kina gaurayawa sosai kina soyawa. Amma karki bari ya soyu sosai, ma’ana dai sama-sama za kina yi masa yana ci har tsawon sati daya ko kuma sati biyu.
Sannan yana da kyau ka yawaita cin kayan itatuwa saboda yana taimakawa sosai wajen bada lafiya, haka zalika a yawaita cin wadannan abubuwan idan da hali.
・ cocumber
・ zuma
・ ayaba
・ kankana
・ da sauran su.
Ga kyautar MAGANIN BASIR kuma.
Duk mutumin da yake shan wahala a bayan gida saboda basir, wani ma sai ya zubar hawaye kafin ya gusar wa kansa, ko kuma ya biyawa kansa bukata ta bayan gida. To ya taimakawa kansa ya samu ;
– Man zaitun
– Garin habbatus-sauda.
Kwaba wadannan abubuwa sai a turashi a cikin duburar sa, yana yin haka kamar kwana biyar ko goma, InshaAllah za’a samu biyan bukata.
Allah yasa mu dace.