Ita wannan cuta ta saurin inzali tana samuwa ne ta hanyoyi da dama, dan kadan daga cikin abin dake saka wannan cuta shine kamar hak.:

Sanyin Mara na Maza Ko mata kansanya saurin inzali.

Yawan yin wasa da gabanka har maniyi ya fita .

Samun dan aike yayin saduwa, maana kafin ku sadu da iyalinka kuyi wani dan wasa da zai kawo shaawarku. [Rashin yin haka kansa saurin inzali].

Wasu kuma kanyi gadonta.

Wasu Kuma damuwa da fargabar cewa zaka Iya biyawa iyalinka bukata ko bazan iyaba.

ABUBUWAN BUKATA

Kubewa Danya 5.
Ruwa Kofi Daya.

YADDA ZAA HADA MAGANIN

Zaa yan-yanka wannan kubewa Sai a kawo ruwa kofi daya a zuba akai sai a tafasa sosai sai tace wannan ruwan sai a kawo zuma a zuba sosai ajuya sai a dinga shan kofi daya safe da kuma yamma.

Insha Allahu wannan matsala zata kau da yaddar Allah.

KO KUMA

Danyar Cita Mai Yatsu.
Masoro.
Kannufari.
Sai a samu wannan cita a dakata sai asamu ruwa a zuba sai sai kawo wannan masoro da kuna kanumfari sai a hadasu a dafa sosai ya dahu. Sai a kawo zuma yadda zataji a zuba shima a dinga shan kofi daya safe da kuma yamma

Insha Allahu wannan Matsala ta kau da yaddar Allah.

BUGU DA KARI:

Zaka iya samun man kanumfari ko Na’a Na’a saika samu ruwan dumi saika wanke azakarinka dashi sosai. Saika kawo wannan man na kanumfarai ko na Na’a Na’a saika shafe zakarinka dashi sosai amma banda kofar da fitsari zai fita, mintuna kadan kafin saduwa da iyalinka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *