Da yawa yawan mutane (musamman mata), suna korafi akan zafi da suke ji a lokacin jima’i ko kuma lokacin da ba’a jima’i dasu. Wannan babbar damuwa ce da mafi yawan lokaci kan addabi ni’imar mace, da kuma hanata sukuni sosai.
Idan mace tana fama da wannan al’amari, akwai abubuwan da ake yi don ganin an rabu dashi na har abada.
Duk mai fama da wannan matsalan zata nemi kayan hadi kamar haka:
– Garin Ganyen kabewa.
– Garin Ganyen zogale.
– Man kadanya
– Garin Majigi.
– Garin Hulba.
Yadda Zaki Hada Wannan Sirri Shine :
Zaki samu kayan hadin sai ki hada su guri guda ki kwaba da man kadanya sai ki dunga shafawa sau uku a rana, duk shafawa sai ki wanke da ruwan dumi zakiyi mamaki qwarai.