Idan har mace tana son kasancewa cikin ni’ima mai dorewa, yadda namiji zai rika kewarta da son kasancewa tare da ita a koda yaushe, akwai hanyoyi daban daban daya kamata abi domin cikar wannan buri.
Zaki nemi kayan hadi kamar haka ;
– Ganyen zogale
-Borkono sansami
– Citta
– Garin kanunfari
– Garin masoro
– Maggie
– Garin tafarnuwa
Yadda Za’a Hada :
Zaki samu wadannan kayan hadi sai ki shanya zogale ki bar ta ta bushe sosai sai ki zuba maggi a turmi ki daka, sai ki zuba sansamin yaji kadan, ki zuba zogalar ki da sauran kaan hadin sai ki daka sosai, sai ki nemi rariyar laushi ki tankade sai ki dunga cin abinci da yajin.