Babu shakka lallai wannan fa’idar da kuke karantawa fa’ida ce wacce al’umma da dama suka yi amfani da ita kuma tayi musu tasiri wajen maganin sha’anin daya shafi jima’i.

Wannan fa’ida tana kara sha’awa, sannan tana kara ruwan maniyyi tana kuma maganin saurarin inzali. Haka nan tana karawa namiji karfin sha’awa, da kuzari, da nishadi, tare da jindadi a lokacin saduwa da iyali.

Abubuwan da zaka samo domin hadawa sune abubuwa kamar haka

1. Ganyen kuka
2. Citta
3. Kanunfari
4. Tafarnuwa

Da farko zaa samu ganyen kuka guda 5 a shanya ya bushe a inuwa,sannan a samu garin citta karamin chokali Garin Tafarnuwa karanin chokali kanunfari chokali 1.

Za’a hade su waje daya a dake su sosai,sai a rika diban rabin karamin chokali ana zubawa a ruwan shayi ba madara ana sha da safe da dare minti 30 kafin a kusanci iyali.

Za’ai wannan hadin na tsawon sati 1 insha Allah za’a samu kuzari karfi da kuma dadewa ana jima’i da rashin saurin kwanciyar gaba.

Allah yasa mu dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *