Duba da kasantuwar yadda ake duba cikar kyawun mace, fuskarta tana ɗaya daga cikin manya manyan jari da ake la’akari da kuma duba a jikinta. Sannan kuma wani abu da yake ɓata fuskar mace shine ƙuraje.

Kurajen fuska suna sanya muni, da rashin kyawu ga ƴa mace, koda kuwa kyakkyawa ce. Don haka duk wacce ke son kurajen dake fuskarta su ɓace ɓat, ga hanyar da zasu bi.

Kayan haɗin sune ;

Lemon tsami
Kurkur
Zuma

Yadda zaki haɗa :

Mace zata wanke fuskarta sosai da ruwan ɗumi, ta goge da tsumma mai tsafta sannan ta tsaga lemon tsamin gida biyu, ta murje fuskarta dasu (akwai zafi kaɗan). Sai bayan kimanin minti biyar ta tashi ta wanke shi da ruwan dumi.

Sannan ta zuba garin kurkur din nan rabin cokali a cikin zuma cokali biyu, ta gauraya ta shafa akan fuskar, ta barshi zuwa kamar minti biyar sai ta wanke. Idan ya bushe ta shafa man zaitun.

In sha Allahu ƙurajen fuskar zasu mutu, kuma duk wani tabo ko baƙi-baƙi zai washe daga kan fuskarta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *