BASIR:- yana samuwa ne a lokacin da jijiyoyin da ke mafitar bahaya suka kumbura daga ciki ko daga waje (wanda muke kira basir mai tsiro), wanda yawancin lokuta hakan na faruwa ne a sakamakon wahala wajen fitar da bahaya.
Basir yafi matsawa wadanda ke da matsalar jinkiri wajen narkewar abinci a ciki, masu ciki da kuma tsofaffi.
Masana kiwon lafiya sun rarraba basir kashi hudu :
1. jijiyoyin dubura sun kumbura amma bai fara tsiro ba, a wannan lokocin mutum zaina digar da jini kadai ne.
2. a wannan lokocin kumburin na iya fitowa (tsiro) lokoci lokoci, musamman lokocin bahaya kuma da kansa yake komawa.
3. idan yakai wannan Matakin yana fitowa akai akai kuma baya komawa da kansa sai dai akomar dashi.
4. a wannan matakin yagama fitowa ko tsiro kuma baya komawa ko kakomar da shi bazai zauna ba zai sake fita.
ABUBUWANDA SUKE HAIFAR DA BASIR :
1- Yawan zaman waje daya.
2- Kiba
3- Juna biyu
4- yinkurin haihuwa.
5- gudawa mai tsanani
6- Yawan yin kashi mai tauri
7- saduwa ta dubura
8- Daukan abubuwa masu nauyin gaske
9- Yawan zama akan toilet na tsawon lokaci
10- Rashin cin Ganye da kayan marmari kamarsu salat da kabeji
ALAMOMIN CUTAR BASUR:
1- Diga ko zubar da jini
2- kumburi ya bayyana daga cikin dubura
3- ciwo sosai amma wassu kan zuwa ba ciwo
4- kaikayi da rashin sukuni .
ABUBUWANDA DA ZASU TAIMAKAWA MAI HEMORRHOID WAJEN WARKEWA.:
Wanda ke da basir kaso na daya da na biyu kan iya maganceshi ta hanyar canza salon rayuwa, daina abubuwan da suke kawoshi, amma in har yakai kaso na uku ko na hudu ko yake zubar da jini,wannan aikin sai anje gun likita.
Ga kadan daga cikin hanyoyin da zasu taimaka wajen warkewa :
1- Gaggauta fitar da bahaya a lokacin da aka ji shi ba tare da jinkiri ba.
2- Shan ruwa a kai a kai.
3- Yawaita cin kayan lambu da kayan itatuwa wadanda ke taimakawa wajen narkar da abinci da wuri su kuma sanya bahaya yayi laushi ya fita ba tare da matsala ba.
4- Yawaita motsa jiki da gujewa zama a guri daya na tsahon lokaci.
5- Gujewa zaunawa a yayin fitar da bahaya kamar yadda ake yi a yawancin bandakuna na zamani. Zama yana hana rage saukin fitar bandaki ya kuma ta’azzara basir. Tsugunne irin na iyaye da kakanni ya fi alkairi
6- Zama a guri mai Laushi a ko da yaushe.
7- sai Neman masana cutar kokuma zuwa asibiti domin baka magunguna da kuma shawarwari.
ILOLIN CUTAR BASUR
GA kadan daga cikin illar da zai iya kawowa mutum :
1.Daskarewar jini a gun, hakan kan iya sa daskararren jinin yaje ya toshe kanana magudanan jini
2. Rubewar jiki, duk inda baya samun jini a jiki akwai ka idajjen lokacin da zaikai ya mutu.
3.Yakan sa kwayoyin cutuka su shiga mutun