Ga wasu kadan daga cikin amfanin sa wajen magance wasu cututtuka guda 10

Ana dafa ganyen zogale da zuma a sha kamar shayi domin maganin Olsa (ulcer).

2- Ana shafa danyen ganyen zogale akan goshi domin maganin ciwon kai.

3- Ga wanda ya yanke ko ya sare ko wani karfe ya ji masa ciwo, zai shafa danyen ganyen zogale inshaAllah jinin zai tsaya.

4- Ga mai fama da kuraje a jiki, ya hada garin zogale da man zaitun ya shafa.

5- Ana sanya garin zogale akan wani rauni ko gembo domin saurin warkewa.

6- Sanya garin zogale a cikin abinci yana maganin hawan-jini da kuma karama mutum kuzari.

KU KARANTA: Zabe: Yan siyasa na kwasar dalibai a matsayin yan bangan siyasa – Sarki Sanusi

7- Ana dafa ganyen zogale tare da sa kanwa ‘yar kadan domin maganin ciwon shawara.

8- Ga mai fama da ciwon ido zai diga ruwan danyen zogale, haka ma mai fama da ciwon kunne.

9- Macen da ke shayarwa ta dafa furen zogale da zuma dan karin nono.

10-Wanda ke fama da yawan fitsari wato cutar Diyabetis ya rinka shan furen zogale da citta kamar shayi.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *