Idan ka karanta ka turawa sauran yan uwa domin su amfana.
Itacen Aduwa sanannen abu ne a kasar Hausawa musamman a karkara – Shi dai ‘ya’yan aduwa ana tsotsan sa ko kuma sha – Man shi da ‘ya’yan shi ana amfani dasu wajen magunguna da dama Itacen Aduwa itace ne dake fidda kwallaye masu matukar amfani a jikin mutum.

Aduwa ta yi matukar suna a kasar Hausawa musamman a karkara. Shi dai wannan ‘ya’yan aduwa tsotsansa akeyi ko kuma sha. Bayan sha da ake yi akan tatsi mai daga kwallan Aduwa.
Ana kiranta da ‘Desert Date’ da turanci. Bincike ya nuna cewa tsoson kwallon nata, da man dake cikin ‘ya’yan ta, suna da muhimmanci sosai wajen bada kariya daga cututtuka a jikin dan adam.

Ga amfanin Aduwa a jikin mutum kamar haka :

1. Aduwa na kawar da cutar asma.
2. Mai fama da atini da zawo zai samu sauki idan ya tsotsi Aduwa
3. Aduwa na kawar da tsutsar ciki.
4. Yana maganin ciwon shawara.
5. Aduwa na maganin farfadiya.
6. Man kwallon Aduwa na rage kiba a jiki, idan ana girka abinci da shi.
7. Yana warkar da ciwo a jiki musamman idan ciwon ya zama gyambo.
8. Man Aduwa na maganin sanyin kashi da kuraje.
9. Yana kawar da kumburi.
10. Yana kawar da matsalar yin fitsari da jini. 11. Man Aduwa na gyara fatar mutum da hana saurin tsufa.
12. Yana kuma kawar da ciwon bugawan

Allah yasa mu dace.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *